Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Duk macen da zata yi aure ya kamata tayi bincike akan namijin da zata aura domin gudun matsala, cewar Rukayya Dawayya

Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood “Rukayya Umar Santa” wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, ta shawarci mata da ke shirin yin aure da su rika yin bincike kafin su fada cikin harkar ta aure.

Advertising

Jarumar Rukayya Umar Santa wacce ta samo sunan “Dawayya” daga wani fitaccen fim dinta mai suna “Dawayya”, ta bayyana cewa a lokuta da dama matan da suka dade ba su samu miji ba sukan yi aure ba tare da sun gudanar da kwakkwaran bincike ba.

Jarumar tana magana ne akan sabon fim dinta mai suna “Ummi Sambo” da aka haska a farkon watan Disambar nan, yayin wata hira da ta yi da wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir.

Sannan jarumar tace, matsalolin da suka fi damun mu sune yawan mutuwar aure da kuma yin aure babu bincike, Dawayya ta kuma bayyana cewa a lokacin da aka tambaye ta jigon labarin fim din na “Ummi Sambo”.

Advertising

Sai tace, muna da manyan ‘yan mata da suka dade ba su yi aure ba, wasu sa’aninsu ma sun kusa aurar da ‘yaya, to wannan abin yana sa kowa yazo miki sai kiyi aure.

Wannan ita ce matsalar dake damun mu, shi ya sa muka dauki wannan bangare a matsayina na mace.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button