Bayan Jama’a sun turawa mawaki “Davido” kudin daya roka ya aikata wani abu da shi wanda Mutane suka shiga dimuwa
Ficaccan Mawakin Kudancin Nageriya “Davido” ya aikata wani abu da Kudaden da bukata Jama’a su tura masa, wanda hakan yasa Mutane suke matukar mamakin abin da ya aikata wda wannan Kudaden.
Idan bazaku manta ba Mawaki “Davido” ya bukaci Masoyan sa da kuma sauran Jama’a da su tura masa da tallafin Kudi a asusun sa na ajiya, inda ya rubuta Lambar asusun nasa lamarin da ya janyo cece-kuce sosai.
Sannan idan baku manta ba mun wallafa musu labarin wasu jaruman Kannywood wanda suma suka bukaci jama’a su tura musu tallafin kudin kamar yadda Mawaki “Davido” ya nema, wanda suma suka rubuta Lambar asusun ajiyar su na Banki domin masu niyya su tura musu.
Bayan Mawaki “Davido” ya nemi a tura masa da Kudaden daga wajan Masoyan sa da kuma Abokan arziki mutane da yawa sun soki wannan batun nasa tare da yin cece-kuce akan hakan, inda ake danganta batun nasa da irin abin da Almajirai suke yi akan tituna wato bara da roko.
To haka suma wadan nan jaruman Masana’antar Kannywood din suka aikata inda suka nemi jama’a su tura musu tallafin Kudaden, inda lamarin ya janyo musu cece-kuce da maganganu daban-daban.
Domin kuji cikekken Labarin akan wannan lamarin zaku iya kallon bidiyon da muka ajiye muku a kasa.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken Labari.