Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Sai da aka bukaci na zama ‘Yar Madigo a wani Fim din Kudancin Nageriya amma naki sabida ina tsaron Allah, cewar Rahama Sadau

Kamar yadda kuka sami Rahama Sadau Ficacciyar Jaruma ce a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood, wanda tayi kaurin suna cikin dan kankanin lokaci sannan kuma tauraruwar ta take haskakawa.

Advertising

A wata shira da Jaruma Rahama Sadau tayi gidan Jaridar “THE GUADIAN” Rahama Sadau ta bayyana cewa, an mata tallar wani Fim na ‘Yan Madigo dake Kudancin Nageriya wanda ake bukatar ta fito a cikin shirin Fim din.

Sun nuna Jaruma Rahama Sadau ta fito a matsayin ‘Yar Madigo a cikin wannan shirin da suka mata talla, amma sai taki amincewa duba da yadda rayuwar da take ba irin tasu bace sannan tayi la’akari sa ita ‘Yar Arewacin Nageriya ce ba ‘Yar Kudanci ba.

Sannan kuma Jaruma Rahama Sadau ta bayyana rungumar da tayiwa Mawakin Kudancin Nageriya wato “Classiq”, inda tace wannan ai abu ne a bangaren aikin ta bai kamata ana tsangwamar ta ba.

Advertising

Sannan kuma Jaruma Rahama Sadau ta sake karkato da hankulan Jama’a akan cewa, shifa tsoron Allah a zuciya yake ba a fili ba don haka bai dace ana mata kallon ‘Yar iska ba sabida tana wasu abubuwan game da harkar ta.

Domin kuji cikekken bayani daga bakin Jaruma Rahama Sadau a shirar da aka yi da ita, sai ku kalli bidiyon da muka saka ta a kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button