Advertising
Advertising
Labarai

Saurayina ne ya yaudare ni yayi Zina dani har na dauki ciki a lokacin da naje dakin sa bashi da lafiya, cewar wata Budurwa

A cikin wani faifai bidiyo da muka ci karo da shi wanda tashar “Alfurqan wal huda” dake kan manhajar Youtube ta wallafa, munji labarin wata matashiyar Budurwa wanda taje buda Saurayinta sabida bashi da lafiya amma sai yaci amanarta yayi Zina da ita.

Advertising

Kamar yadda Budurwar take fadin cewa: Saurayin nata ne ya sanar da ita cewa bashi da lafiya ita kuma sai ta masa addu’ar Allah ya bashi lafiya, bayan haka sai ya bukaci taje wajan sa domin ganin yadda yake amma sai Budurwar taki yarda.

Amma Saurayin nata sai da yasan yadda yayi ya shawo kan ta inda Budurwar tayi tattaki har zuwa kofar gidan su Saurayin nata, da zuwan Saurayin nata sai ya bukaci su shiga cikin gidan tare nan ma taki yarda amma sai da yasan yadda yayi ta shiga gidan.

Da shigar su cikin gidan sai ya kaita dakin da yake kwana yayi ta mata dadin baki tare da wasu maganganu daga nan kuma har ya sami damar da yayi Zina da ita.

Advertising

Bayan wasu ‘Yan watanni da faruwar wannan al’amarin sai Budurwar ta fara jin wani yayi wanda bata saba ji ba, inda a karshe aka yi bincike sannan aka gano cewa tana dauke da ciki.

Daga nan aka fara zuwa wajan iyayan Saurayin nata domin asan yadda za’a yi a sami mafita akan wannan al’amrin, inda abin yaci tura har ma ta kaisu ga zuwa wajan ‘Yan sanda har lokacin da Budurwar ta Haihu.

Domin kuji cikekken bayani daga bakin wannan Budurwar sai ku kalli bidiyon dake kasa kuji yadda tayi bayanin duk abin da ya faru tsakanin ta da wannan Saurayin nata.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button