Labaran Kannywood

Allahu Akbar Khulu Nafsin Za’ikhatul Mau: Sani Garba SK yayi cikekken bayani akan masu yada labaran cewa ya Mutu

Kamar yadda kuka sani a yanzu haka ana tsaka da yada labarai akan mutuwar Jarumin Masana’antar Kannywood Sani Garba SK.

Bayan wallafa wadan nan labaran da ake sai muka sami wata bidiyo wanda Jarumi Sani Garba SK ya bayyana a ciki yana bayani akan abin da yake damun sa, da kuma neman taimakon da yake a wajan al’umma akan rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sannan Jarumi Sani Garba SK yayi gargadi ga mutanen da suke yada labaran karya a kafafan sada zumunta akan sa, domin hakan da suke yana janyowa maganganu kala-kala tare da cece-kuce akan sa.

Kana ya kara da cewa: Ita Mutuwa dole ce baka isa ka wuce lokacin ka ba kuma dole ne sai kowa dake fadin Duniyar nan ya Mutu, sannan ya kara godewa masoyan sa da kuma abokan sana’ar sa ‘Yan Kannywood da suka taimaka masa akan rashin lafiyar da yake fama da ita.

Ga bidiyon nan domin kuji cikekken bayani daga bakin Jarumi Sani Garba SK.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button