Ashe wannan dalilin ne yasa Mutane suke cece-kuce da maganganu masara dadi akan jarumi Lawan Ahmad da Garzali Miko
Kamar yadda muka sami wani labari a ayu akan wasu daga cikin Jaruman Masana’antar Kannywood wanda suka aikata wani tsari irin na Almajirai wajen neman abinci ko kudi, to suma haak Jaruman suke suke rokon Mutane su tura musu da kudi.
Jaruman na Masana’antar Kannywood sun fidda wani tsari wanda kowa yake ganin sun fara bara da roko kamar yadda Almajirai suke, inda suka fidda sabon tsari na rokon mabiyan su a shafin su na sada zumunta domin su tallafa musu da wani kudi.
Kamar yadda wasu suke fassara bara ko roko suna ganin yin su mummunan dabi’a ce wanda mutane zasu yiwa masu yin su kallon masara aikin yi da kuma mutuwar zuciya, inda wasu ma suke yaki da ita domin ba aba ce wanda ta dace ba.
Duk mutanen da suke yin bara suna amfani da sunan Manzon Allah S.A.W inda suke cewa a basu don Annabi, sannan kuma babban abin dubawa anan shine Manzon Allah S.A.W bai taba yin bara ba inda ma yayi nuni da cewa ba dabi’a ce mai kyau ba.
Baya ga haka kuma babban abin dubawa shine duk masu yin bara suna dauka kamar wata aba ce da take cikin addini, domin suna ganin kamar yin bara ko roko abu ne mai kyau.
Sannan duk mutumin da ya kasance yana bibiyar kafafan sada zumunta yasan abin da ya faru a wannan lokacin domin wani shahararran Mawakin Kudancin Nageriya mai suna “Davido” ya roki mutane da su tura masa kudi.
Inda yawancin mutanen Kudancin Nageriya sun fi zagin duk wasu wanda suke bara ko roko, sai kuma aka samu wani shahararran Mawaki dan cikin su ya aikata abin da suka tsana.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken labari kan wannan cece-kucen da yake faruwa akan karuman kannywood wanda suka roki mutane da su tura musu kudi.
Danna nan domin ka kalli bidiyo.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇