Jaruman Kannywood sun hargutse da murna da farin ciki akan abubuwan abin alkairin da Senator Barau I. Jibrin ya basu
A yau ne muka sami labarin wani abin alkairi da Senator Barau I. Jibrin ya yiwa Jaruman Masana’antar Kannywood, inda suka cika da mamakin wannan abin alkairin da ya musu.
Kamar yadda Jarumi kuma Darakta a Masana’antar ta Kannywood wato “Falalu A Dorayi” ya wallafa labarin a shafin sa na sada zumunta Instagram, yana mai cewa.
Muna godiya da sakon abubuwam alkairin da aka bawa al’ummar Kannywood.
Falalu A Dorayi ya wallafa abubuwan abin alkarin da aka basu kamar haak.
Motoci Guda 17
Babura 100
Komfuta 80
Kamara 5
Generator 5
Kayan Studio 5
Kayan Light 5
Dudu 30,000 Mutum 100
Dudu 20,000 Mutum 100
Kujerar Hajji Mutu 1
Sannan Jarumi Falalu A Dorayi ya jara da cewa:
Muna godiya ga
Murtala Alassan Zainawa
Isyaku Balan (Barau Maliya)
Sani Ali Abubakar (Indomie)
Ali Nuhu
Abba Maikatala
Abdul A.P
Adam A. Zango
Mustapha Nabursaka“
Daga karshe yayiwa Senator Barau I. Jibrin kyakkyawar addu’a akan abubuwan abin alkairin da ya bawa al’ummar cikin Masana’antar Kannywood, inda yake cewa.
Allah ya yiwa rayuwa albarka, Senator Barau I. Jibrin (MALIYA).