Yanzu Jaruma Umma Shehu ta tonawa wasu mutane asiri da suke neman bata mata suna a Duniya
Ficacciyar Jarumar Masana’antar Kannywood Umma Shehu wanda take sharafinta a cikin shirin nan mai dogon zango wato “Gidan Badamasi” wanda Tashar Arewa24 take haskawa.
Jarumanr ta bayyana a cikin wata bidiyo tana wayarwa da jama’a kai sabida wasu mutane da suke amfani da sunan ta suka zaluntar jama’a, jarumar ta bayyana cewa bata amfani da kafar sada zumunta ta Faccebook.
Sannan kuma duk wanda yaga wani sunan ta a kafar sada zumunta ta Facebook to ba ita bace domin tana samin korafe-korafe daga wajan mutane akan cewa, tana yaudarar mutane game da kasuwancin ta da take gudanarwa a kafar sada zumunta ta Facebook.
Sannan kuma ta sake yin jan kunne ga mabiyanta da cewa, kwata-kwata bata amfani da shafin Facebook shafukan da take amfani dasu basu wuce, Instagram da TikTok ba.
Wadannan sune kawai shafukan sada zumunta da Jaruma Umma Shehu take amfani da su domin gudanar da kasuwancin ta cikin sauki, sannan kuma duk wani shafi da mutum ya gani na daban to gaskiya ba nata bane kuma karya aminta da shi.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin Jaruma Umma Shehu akan mutanen da suke amfani da sunanta shafin Facebook suna yaudara jama’a.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani daga bakin Jaruma Umma Shahu.