Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

A yanzu bana jin dadin shirin Fim idan ba Jaruma Nafisa Abdullahi sabida mun shaku da ita a shirin Labarina, cewar Mahmud Labarina

Ficaccan Jarumin shirin Labarin mai dogon zango Nuhu Abdullahi wanda aka fi sani da Mahmud ya bayyana cewa, a yanzu yafi jin dadin shirin Fim da Jaruma Nafisa Abdullahi wacce ake kiranta da Sumayya Labarina.

Advertising

Jarumi Nuhu Abdullahi wato Mahmud ya bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da BBC Hausa inda yake fadin cewa, sabida shakuwar da sukayi da Jaruma Nafisa Abdullahi ne yasa a cikin shirin Labarina yasa a yanzu bayajin dadin shirin Fim sai da ita.

Sannan kuma a lokacin da suke tattaunawa da BBC Hausa a wannan shirin nasu mai suna na daga bakin mai ita, ya bayyana tarishin rayuwar sa tare da kalubalen da ta fuskanta game da rayuwar sa.

Wanda a yanzu ma haka Jarumin yana fuskantar wasu kalubale dangane da yadda yake gudanar da haskokin sa na Fina-Finai, musamman shirin Fim din da ya shahara a ciki wato Labarin.

Advertising

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin Jarumi Mahmud a lokacin da suke tattaunawa da BBC Hausa akan tarihin rayuwar sa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekkiyar shirar da aka yi da shi.

https://youtu.be/8tAIVKtvrlM

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button