An bayyana gaskiyar al’amari akan wasu Jaruman Kannywood da sukayi soyayya mai zurfi amma basu yi aure ba
kamar tadda kuka sani Masana’anyar Kannywood tana dauke da Jarumai Maza da Mata da dama wanda a ciki ake samun wadan dasuke soyayya daga bisani kuma suyi aure.
A cikin wata bidiyo da muka samu a yau wanda Tashar “Gaskiya24 Tv” ta wallafa ta jero wasu daga cikin Jaruman Manasa’antar Kannywood wanda sukayi soyayya mai zurfi amma basu sami damar yin aure ba.
Inda a farko aka fara bayanin soyayyar Jaruma Nafisa Abdullahi da Jarumi Adam a Zango wanda a shekarar 2015 Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyanawa Jarumi Adam a Zango soyayyar ta, inda ta bayyana masa soyayyar da take masa ta shafin Instagram.
Sannan kuma Jaruma Nafisa Abdullahi tayi musu addu’a ta gari da cewa, Allah ya zaba musu abin da ya fi alkairi a tsakinsu ita da Jarumi Adam a Zango.
Tun kafin soyayyar Jarumi Adam a Zango da Jaruma Nafisa Abdullahi tayi karfin da al’umma zasu sani, suke gudanar da soyayyar su bisa jin dadi da kuma farantawa juna rai, a lokacin sa Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyaanwa Jarumi Adam a Zango cewa tana son sa shima ya maida mata da amsa kamar haka.
Jarumi Adam a Zango ya fadi cewa: Yayi matukar farin ciki da abokiyar aikin ta bayyana masa cewa tana matukar kaunar sa, inda shima yace yana matukar kaunarta sannan kuma Allah ya zaba musu abin da ya fi alkairi a tsakanin su.
Zaki iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken labari game da Jaruman Masana’antar Jannywood wanda sukayi soyayya mai zirfi amma daga karshe basu yi aure ba.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken labarin.