Bai kamata Musulmin kirki ya zabi Sanata Barau Jibrin a matsayin Gwamnan Kano ba, Daga indabawa Aliyu Imam
Bai kamata Musulmin Kirki ya zabi Sanata Barau Jibrin a matsayin Gwamnan Nihar Kano na. Daga (Indabawa Aliyu Imam)
Duk Jam’iyyar data yi gangancin tsayar da Sanata Barau Jibrin matsayin Gwamnan Kano ta shirya rungumar mummunan kayi, domin da sanyin safiya a kayar da ita
Sanata Barau bai cancanci zama ko Kansila ba balle Gwamnan babban gari mai albarka irin Kano.
A labarin da na gani jiya wanda ya yi matukar sosa min zuciya shi ne, Sanata Barau ya tara ashararun yara ‘yan fim masu lalata tarbiyya ya kashe musu fiye da miliyan dubu daya, (Bilyan daya) ta hanyar raba musu motoci
guda ishirin da takwas da babura guda d’ari.
Sannan ya raba musu kyamarori masu tsada da fitilolin aiki da na’urorin kara sauti da kwamfiyotoci da miliyoyin kudade, wanda rahotanni suka ce kimanin mutum dari biyar da tamanin ne a masana’antar kannywood suka amfana da wannan rabo.
Ba haushi nake ba an kara wa masu karfi karfi ba Takaicina shi ne wannan abu ya faru ne a dai-dai sanda marasa lafiya ke mutuwa a asibitici saboda rashin kudi. Ya faru ne a sanda talakawa ke mutuwa saboda yunwa,
Ya faru ne sanda kauyen da aka haifi Sanata Barau ke fama da matsanancin rashin ruwan sha har sai sun yi tafiya mai nisa suke samun sa.
Ga nagartattun matasa nan marasa aikin yi wadanda ke fafutukar neman jari, ga wurare nan da dama da suke bukatar ginin makarantun addini da na zamani don
ilmantar da al’ummarsu, Kauyuka nawa ke bukatar asibitoci a Kano ta Arewa?, Mata nawa ne ke mutuwa a yayin haihuwa saboda rashin asibiti?.
Marayu nawa ne ke bukatar kulawa don rayuwa ingantacciya?, Batutuwa nawa ne na addini da suke bukatar tallafi?, Babu aiki guda da Barau ya yi cikin abubuwan da na lissafa amma ya je ya tara karuwai da
‘yan daudu yana kashe musu kudin al’umma saboda rashin sanin abin da yake yi.
Akwai Dalibin da ya ce sun yi sauka a makarantarsu sun tura wa Barau katin gayyata da neman tallafin ginin makaranta ya karba ya kuma yi alkawarin zuwa amma
bai je ba bai kuma tura wakili ba, Shekara d’aya baya ma ina gidan wani babban Malami a Kano na ji ana zancen ya yi alkawarin zai gina masallaci amma bai gina ba.
Barau Shekarun da ka shafe ba ka tsinana wa yankinka wata tsiya ba a Majalisar dattijan ma dumama kujera ka ke yi, ba ka tsinana wa mutanen Kano komai ba amma ka kwashi kudin al’umma ka je kana raba wa ‘yan fim.
saboda su yi maka tallan takararka da ace kana da zurfin tunani ko mashawarta nagari da za su ce maka mu’amala da ‘yan fim bata ka zai yi a idon jama’ar Kano ba ya haifar
maka da farin jini ba.
Ko Sanata Shekarau din da kake masa raragefe don ya goya maka baya ka yi takarar Gwamna mutum ne mai kishin addini da tarbiyyar al’umma, mafi yawan mabiya Malam Shekarau suna goyon bayansa ne saboda addini da kuma aiki tukuru da ya yi a shekarun baya wajen kakkabe wadannan yara ‘yan fim masu dabbaka shaidanci da yahudanci.
Barau zai yaudari kansa ne ma ya ce wai Malam Shekarau zai goya masa baya ni ba dan siyasa ba ne amma na rantse da sarkin da ke busa min numfashi sai mun yaki Barau, da duk wata dama da muke da ita a
matsayinmu na ‘yan jarida marubuta ba ni kadai ba duk wani wanda ke da kishin addini wajibi ne a kansa ya yaki Barau.
Duk wanda ke fifita mutanen banza shi ma na banza ne
‘Yan fim yaran da suka yi kaurin suna wajen koyar da alfasha, zinace—zinace, shaye—shaye da dabbaka yahudanci, da kuma rushe tarbiyyar addinin musulunci Da yawan matan cikinsu ‘yan siyasa ne da masu hannu da shuni ke lalata da su suna ba su kudi.
An fad’a min wani babban dan wasa a cikinsu wanda ya yi kaurin suna wajen kawalci, an ce min har kawalcin madigo da luwadi yana yi.
Isu-isu ma fitowa suke su fallasa irin fasikancin da suke yi a junansu na zinace-zinace, madigo da luwad’i, fasikancin wadannan yara na daga sababin halin damuka sami kanmu na musibu kuma dama Allah da manzonsa sun fada mana.
A wata ziyara da na ziyarci Hukumar tace fina-finai shugaban hukumar Malam Ismeil afakallah ya bayyana min irin kalubalen da yake fuskanta daga wadannan yara, laifinsa shi ne kawai ya ce sai an yi gyara an bi dokar musulunci Irin labaran da ya ba ni na munanan ayyuka da wadannan yara ke aikatawa bakina ba zai iya furta su a nan ba.
Shi yasa suke ta shirya masa bita da kulli kamar yadda suka yi wa Malam Abubakar Rabo Abdulkarim wanda laifinsa shi ma bai wuce na kawo musu gyara ba, dogaro da wannan Sanata Barau ba mutumin kirki ba ne kar wani mutumin kirki ya zabe shi.
Domin idan yaci zai bar ‘yan fim su ci karansu babu babbaka suci gaba da yada alfasha da fasikanci suna lalata tarbiyya, wanda hakan zai haifar da wanzuwar musiba cikin al’umma wannan kalubane ne ga Malaman jihar Kano da masu fada aji kar su yarda su goyi bayan Barau Jibrin ba mutumin kirki ba ne ba shi da kishin
addini.
Insha Allah Barau yaci taliyar karshe Allah kar ya ba mu shugabanni masu hidimta wa mutanen banza irinsu Barau Jibrin.