Da dumi-dumi ‘Yan Sanda sun kama Mutumin da yake yaudarar ‘Yam mata yana saida musu da kayan ado na bogi
A yanzu ne muka sami wani labari daga shafin BBC Hausa na Instagram inda mukaga sun wallafa labarin wani mutumi da ‘Yan sanda suka kama shi da aikata wani babban aifi.
‘Yan sanda sun kama mutumin ne da laifin zambatar al’umma talatin da bawai 37 a yanar gizo-gizo wato Intanet, inda mutumin yacu amanar su ya sayar musu da gidan sauro a maimakon atamfa wanda mata suke saya domin suyi ado da ita.
Bayan yaudara su da mutumin yayi akan sai da musu gidan sauro a maimakon atamfofi har da sayar musu lesussuna wanda shima da gidan sauron aka yi shi.
‘Yan sandan sun bayyana cewa: Matashin mai suna Aliyu Hussaini dan shekara ashirin da biyar 25 ya bude wani shafi a dandalin sada zumunta na Facebook, inda yake tallata hajar sa ta yadudduka kala daban-daban.
Bayan an bayyana ta’asar da wannan mutumin yake nan da nan jama’a suka fara tofa albarkacin bakin su tare da fadin maganganu daban-daba akan abin da wannan mutumin yake aikatawa na rashin imani ga mutanen da yake saidawa kayayyakin bogi.