Jarumin shirin Dadin Kowa Nazir ya bayyana gaskiyar al’amarin abin dake tsakanin sa da Alawiyya, domin jama’a suna zaton wani abu
Ficaccan jarumin shirin Dadin Kowa mai dogon zango wanda Tashar Arewa24 take haskawa a duk sati wato Ahmad Bello wanda kowa yafi sanin sa da Nazir, ya bayyana wani gadkiyar al’amarin dake tsakaknin sa da Alawiyya.
Nazir ya bayyana hakan ne a shirar da suka yi da gidan Jaridar BBC Hausa a wannan shirin nasu na Daga bakin mai ita, inda ya bayyanawa al’umma gaskiyar al’amari akan abin dake tsakanin sa da Alawiyya ta cikin shirin Dadin Kowa mai dogon zango.
A cikin wannan shirar tasu da BBC Hausa Nazir ya fadi asalin inda aka haife shi inda yake bayyana cewa, an haife shi ne a garin Jos sannan kuma yayi tashi yayi rayuwar sa a garin Jos, sannan kuma yayi makarantar Pramary da Secondary duka a garin Jos.
Sannan kuma ba yanna cewa: Yanajin yarurruka da dama kamar su, Turanci, Hausa da kuma Fulatamci da dai sauran su, haka kuma ya bayyana cewa tun yana karamin yaro yake sha’awar shifa harkar Fina-Finan Hausa.
Baya ga haka ya bayyana wasu al’amura da dama da suka shafi rayuwar sa tun yana karamin yaro har kawo zuwa wannan lokacin da ya girma.
Domin kuji cikekkiyar shirar da BBC Hausa tayi da Jarumi Nazir na cikin shirin Dadin Kowa mai dogon zango akan tarihin rayuwar da, sai ku kalli bidiyon da muka saka a kada.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.