Advertising
Advertising
Labarai

An yankewa dan wasan Kwallon kafar Real Madrid Karim Benzema hukuncin zama a gidan gyaran hali sabida bidiyon Lalata da yayi yunkurin nunawa Duniya

Dan wasan kwallon kafar Real Madrid wato “Karim Benzema” an kama shi da laifin cin amana game da wani batu da ya shafi faifai bidiyon lalata, na wani tsohon dan wasan kwallon kafa na Faransa wanda suka taka leda tare.

Advertising

Bayan kama dan wadan kwallon kafar da aka yi wato “Karim Benzema” na yake masa hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekara daya 1, sannan kuma zai biya tarar Dala $84,000.

Dan kwallon kafa na Real Madrid “Karim Benzema yana da shekara talatin da uku 33 a duniya sannan yana cikin wasu mutane da aka gurfanar da su a watan da ya gabata, sabida karbar kudi a hannun Mathieu Valbuena sannan kuma yayi ikirarin cewa zai bayyana bidiyon ga Duniya domin kowa ya gani a shekarar 2015.

Advertising

Wannan badakalar ta tayar da kura sosai a Faransa inda dukkan nin ‘Yan wasan kwallon kafa aka dakatar da su daga bugawa Faransa wasa.

Bbchausa ta ruwaito Masu gabatar da ƙara sun ce Benzema ya tursasawa Valbuena ya biya masu ɓata sunan waɗanda kuma ya haɗa baki da su.

Benzema ya sha musanta laifin da ake tuhumarsa yana mai jaddada cewa ya yi ƙoƙarin taimakawa Valbuena domin kawar da bidiyon.

Ɗan wasan na Real Madri ba ya cikin kotun Versailles lokaci da aka zartar masa da hukuncin, haka ma Valbuena wanda ke buga wa Olympiakos ta Girka wasa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button