Kalli sabon shirin da aka fidda a yanzu mai suna “Daga masu kallon Izzar so” Episode 1, daga tashar BAKORI TV

A yanzu haka akwai wani sabon shiri wanda ake harka shi a tashar “BAKORI TV” wanda a cikin tashar ake haska shirin “IZZAR SO” mai dogon zango, sabon shirin mai suna “Daga masu kallon izzar so” an fara haska shi ne a tau ranar Talata.
Jarumin shirin Izzar so Lawan Ahmad ya bayyana cewa: Wannan sabon shirin nasu mai suna “Daga masu kallon Izzar so zai kawatar da Jama’a sosai, kamar yadda shirin Izzar so yake kawatar da Jama’a masu kallo.
Sannan kuma Jama’a da dama sun karbi shirin Izzar so hannu biyu wanda tun farko alamu sun bayyana Jama’a na suna son shirin Izzar so matuka, sabida yadda yake samin dinbin al’umma masu kallo.
Da alamu wannan sabon shirin mai suna Daga masu kallon Izzar so zai sami karbuwa a wajan Jama’a da dana, domin za’a shirya shirin cikin tsari kamar yadda aka shirya Izzar so.
Ga sabon shirin nan dai mai suna “Daga masu kallon izzar so Episode 1 Original”.
Ga shirin nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.