Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yadda ‘Yam Mata da dama suka fashe da kuka sabida tausayi lokacin da suke sauraron wakar shirin Labarina “Rayuwa Kaddara ce”

Kamar yadda kuka sani a cikin shirin Labarina mai dogon zango an rera wata waka wanda da dauki hankulan Jama’a da dama, wanda har ma wakar takan sa masoya da dama kuka sabida kalaman da ake fada a cikin wakar masu ratsa zuciya ne.

Advertising

Wakar mai suna “Rayuwa Kaddara ce” ta shahara wanda a yanzu ba ko wace waka ce ta sha gaban ta ba domin sabida ko Saurayi da Budurwa ne suka rabu da junan su, to muddin idan daya daga cikin su yake sauraron wannan wakar ta “Rayuwa Kaddara ce” zai iya yin kuka.

To a yau kuma mun sami wata bidiyo wanda muka ga wasu mata suna kuka sosai ta dalilin sauraron wannan wakar mai taken “Rayuwa Kaddara ce” wanda aka rera ta a cikin shirin Labarina mai dogon zango.

Shahararran Mawaki Salim Amart shine ya rera Wakar inda ta sami karbuwa a wajan Dubbannin al’umma kuma tayi farin jini sosai.

Advertising

Daga cikin Matan da suka yi kuka dalilin sauraron wannan Wakar har da wasu daga cikin Jaruman Masana’antar Kannywood Mata, sannan kuma akwai wasu Maza wanda suma zuciyar su ta karaya suke zubda hawaye a lokacin da suke sauraron Wakar.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuga yadda suke sauraron Wakar “Rayuwa Kaddara ce” kuma suke zubar da hawayen su sabida tausayi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button