Advertising
Advertising
Labarai

Ai’sha Yesufu ta sake aika zazzafan martanin da kowa yayi mamaki ga Shuwagabanin Arewa da suna ji ake kashewa Al’umma

Da farko Ai’sha Yesufu tayi sallama ga al’ummar Musulmai sannan tace abin da yake zuciyar ta zata fade shi, inda ta kara da cewa wanda zai zageta bata damu ba dama sun saba.

Advertising

Nan take ta fara da cewa: Ina munafukan Arewa suke ana nan ana rugugu da Arewa ana ta kakkashewa Mutane sannan ana konewa gonakin Mutane, tare da yin abin da aka dama a Arewa.

Ta kara da cewa: Amma ban munafinci baza’a yi magana ba kuma wai dan Arewa ne yake kan karagar mulkin Kasar Nageriya amma anji kunya wallahi, sannan kuma kun bawa Addinin Musulinci kunya.

Advertising

Domin Addinin Musulin bai sa muga gaskiya sannan kuma muki fadar ta ba domin Musulinci an san shi da gaskiya, amma sabida kabilanci ta juya ku ta mamaue ku ta maida ku wani abu daban amma bazaku fito kuyi magana ba, kuma munafukan banza dana wufi suna nan bazasu yi magana ba.

Sannan Ai’sha Yesufu tace: Duk wanda bai dauki wannan bidiyon nata ya yadashi ba to bai cika haifaffe a wajan Mahaifiyar sa ba, kuma ta bada damar a yada bidiyon nata a kowane kafafan sada zumunta domin taje ga shuwagabannin Arewa.

Shi yasa muma muka dauko bidiyon nata daga Tashar “Kundin shahara” dake kan manhajar Youtube, muka wallafa ta a cikin wannan site din nasu domin kuji bayanin da take akan Shuwagabannin Arewacin Nageriya.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji yadda Ai’sha Yesufu take aika zazzafan martani ga Shuwagabannin Arewacin Nageriya.

https://youtu.be/OkML8C7wF78

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button