Advertising
Advertising
Labarai

Amfanin Lemon Tsami ga Namiji ko Mace wanda suke da karancin Maniyyi da kuma illar sa a jikin dan Adam

A Bincike da masana suka yi ya nuna cewa: Akwai alaka mai karfi tsakanin lemon tsami da maniyin namiji musamman ta bangaren samar da kwan halitta yana taimakawa wajen kara karfin gudun maniyi.

Advertising

Akwai sinadaran “Vitamin C da thiamine” a cikin lemon tsami wanda ke bunkasa kwan haihuwa ta hanyar kara
karfi ga maniyi, dangane da ikirarin wasu na cewar lemon tsami na tsinka maniyi, “Hajiya Jummai Hassan” wacce kwararriyar likita ce kan abinci a asibitin Wuse a Abuja ta karyata hakan.

Ta bayyana cewa: Ruwan lemun tsamin da ake matsawa a ruwa ko a shayi a sha bai kai yawan da zai tsinka maniyi ba illa ma zai gyara da inganta shi, sai dai wani bincike da aka gudanar a kasar Australia na nuni da cewa, shan lemon tsami mai yawa a lokaci daya yana tsinka maniyi hakan illa ne ga iyalan da ke son he da tazararhaihuwa.

Ga hanyar da za’a bi domin ayi amfani da Lemon tsami yadda ya dace.

Advertising

Matakin farko na amfani da lemon tsami shine: Yin amfani da shi a lokacin da aka yanka shi za’a iya amfani da shi a ruwa, salads, zuma ko a cikin shayi, wani lemon ko cinnamon sai ka samu ruwa kofi daya ka matsa lemun tsami guda daya, idan kana 50 ka hada da zuma, irin wannan hadin ana so a shashi kafin ayi karin kumallo.

Sannan kuma: Bincike ya nuna cewa cin yayan itatuwa masu dauke da sinadarin “Vitamin C” kamar lemon tsami yana rage hatsarin kamuwa da cutar zuciya ko shanyewar
rabin jiki.

Baya ga haka Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa: Duk da tarin amfanin lemon tsami ga lafiyar dan Adam hakan baya hana lemon tsamin zama mai illa a jiki ba, musamman ga masu ciwon gyambon ciki Kasancewar lemon tsami na dauke da sinadarin asid mai yawa.

Kuma gyambon ciki (ulcer) na gaba da asid hakan na iya daga ciwon da zaran mai dauke da shi ya sha lemon tsami, Kwararriyar likitar abinci ta asibitrin Wuse Hajiya
Jummai ta bayyana cewa.

Lemon tsami yana illa ne kawai ga masu dauke da cututtukan da ke adawa da asid a cikin su sannan kuma ga mutanen da jikinsu ke zabar nau’ikan abincin da suke so, da yawansu lemon tsami na sanya su yin amai ko zafin zuciya da kumburin jiki a cewar mujallar Healthline.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button