Advertising
Advertising
Labarai

Ya kamata shugaba Muhammad Buhari ya dawo mana da Babba Kyari domin a daina garkuwa da Mutane, cewar Datti Assalafy

Kamar yadda kuka sani a wannan lokacin ana yawan tarewa matafiya sannan kuma ayi garkuwa da su inda masu garkuwa da Mutanen suke kashewa wasu daga cikin wandan da suka kama, sannan kuma su ajiye wasu domin a biya su kudi sannan ku sake su.

Advertising

A yau kuma mun sake samin wani labarin akan masu garkuwa da Mutanen inda suka jera kwana uku 3 suna tarewa Mutane suna garkuwa da su, a tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka kashe wasu daga cikin wadan da suka kama.

Masu garkuwa da Mutanen suna cin karan su babu babbaka a wanda har Sojoji ma basu tsira ba a wannan hanyar, to zuwa nan gaba ma ba’a san mai zai faru ba wanda a yanzu hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama tarko ga masu garkuwa da Mutane.

Advertising

Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ka sani cewa mutum daya ne cikin jami’an tsaron Nigeria masu garkuwa da mutane suke jin tsoro shine DCP Abba Kyari.

Anyi taron dangi an yiwa DCP Abba Kyari mummunan sharri aka dakatar dashi domin a gudanar da bincike, a lokacin da tsaron Nigeria ke matukar bukatarsa, kusan wata biyu da kammala bincike ba’a samu DCP Abba Kyari da laifi ba, sannan an gagara dawo dashi bakin aiki, me hakan yake nufi?.

Muna ji muna gani sai anyi yunkurin dawo dashi aiki sai a shashantar da al’amarin, shin ba’a so DCP Abba Kyari ya kalubalanci masu garkuwa da mutane ne ko kuma cin amanar tsaron kasa ake nufi?.

Shin da cigaba da dakatar da DCP Abba Kyari da kuma dawo dashi bakin aiki don Allah wanne yafi alheri ga tsaron Nigeria?.

Abinda aka yiwa DCP Abba Kyari ya karya lagon duk wani jami’in tsaro a Nigeria da yake da zuciyar jarunta, ba kowani jami’in tsaro bane zai yadda ya sadaukar da lokacinsa da rayuwarsa kamar yadda Abba Kyari yayi saboda ganin irin wulakanci da neman tozarci da aka yiwa Abba Kyarin.

Tun da aka dakatar da DCP Abba Kyari matsalar garkuwa da mutane cigaba da karuwa yake kuma Abba Kyari kadai ya san hanyoyin sirri da yake bi ya karya kashin gadon bayan manyan barayin kasarnan masu garkuwa da mutane, amma saboda makirci aka masa sharri bincike ya wankeshi daga zargi amma an gagara dawo dashi.

Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari kai Allah Ya bawa karfin iko, yau idan kace kar a wuce minti 30 ba’a dawo da DCP Abba Kyari bakin aiki ba an gama.

Baba Buhari don Allah Ka sa baki a dawo mana da DCP Abba Kyari, ko hanyar Abuja zuwa Kaduna kadai tana matukar bukatar gudunmawarsa, balle sauran bangarori da ake fama da matsalar garkuwa da mutane.

Muna kira ga ‘yan uwa na social media, don Allah mu juya alkalamin rubutun mu wajen tunatar da shugaba Buhari ya sa baki a dawo da DCP Abba Kyari bakin aiki,

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button