Advertising
Advertising
Labarai

Yadda Jami’an tsaro da sauran Al’umma suke guduwa domin tseratar da rayuwar su yayin da aka kai hari kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Kamar yadda kuka sani Kasar Nageriya a yanzu tana cikin tashin hankalin da Al’ummar cikin a kullun suna cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali, musamman Al’ummar da suke Arewacin Kasar.

Advertising

To a yanzu ne muka sami wata bidiyon wanda Tahsar “Tsakar gida” dake kan mangajar Youtube ta wallafa, inda a cikin bidiyon zakuga yadda Al’umma suka shiga cikin tashin hankali inda ma suke guduwa cikin Daji domin tseratar da rayukan su.

Wannan tashin hankalin ya same su ne a ranar Larabar data gaba ta wato jiya, wanda harin da aka kai bai kyale Jami’an tsaro ba balle Al’umma da basu da wani katabus.

Inda zaka ga Soja da kan sa yana guduwa domin ya tseratar da ran sa a lokacin da aka kai wannan mummunan harin, sannan kuma wannan shi ne hari na uku 3 da aka kai a cikin sati daya.

Advertising

A wani labari da aka bayyana an gano cewa, ‘Yan kungiyar Boko Haram ne suke kai wa wannan harin dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda aka tabbatar da ba’a san yawan Jama’ar da aka sace a ranar farko ba.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button