‘Yan iskan Maza ne suke yaudarar mu suke bata mana suna shi yasa bama Aure da wuri, cewar Jaruma Zuwaira Abdussalam
Ficacciyar Jarumar Masana’antar Kannywood “Zuwaira Abdussalam” ta bayyana Mazan da suke zuwa neman Auren ‘Yam Fim da cewa, dukkan su mayaudara ne.
Zuwaira Abdussalam ta kasance Tsohuwar Jaruma a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood, inda ta bayyana wannan batu nata a lokacin da suke tattaunawa da wakilin Jaridar Damukaradiyya akan zargin da ake wa ‘Yam na ruwan ido wajan zaben Mazan da zasu Aura.
Amma Tsohuwar Jarumar ta bayyan cewa: Gaskiya ni ban yarda da wannan zaben ba sabida mu Mata da muke cikin harkar Fim, idan ka kula mafi yawancin Mazan da suke zuwa neman Auren mu sune suke zuwa sa yaudara ba wai mune bama son Auren ba.
Sannan ta kara da cewa: Mazan da suke zuwa kallon a cikin shirin Fim sune suke zuwa da yaudara wajan mu sabida sai suzo su mana karya da su wasu ne, amma daga baya sai ka gane da haka bane sai kaga Mutum ya sanja daga matsayin da ya fada maka.
Daga baya sai kaga yazo da wata shiga ta daban sannan kuma da zarar ka gano su nan take sai su rabu da kai su kauce, amma sai ana dauka mu Matan ne muke yaudara su don haka yaudara ba halin mu bane.
Daga karshe Tsohuwar Jaruma “Zuwaira Abdussalam” tayi kira ga al’umma da su rinka yi musu adalci akan abin da suke fada game da su, domin suna ‘Yam Fim din ‘Yaya ne kamar kowa sabida haka ya kamata ana musu adalci.