Matashin da yayi Wuff da Baturiya mai shekara 75 a Duniya ya bayyana irin kalubalen daya fuskanta lokacin auren nasu
Wani Matashi mai suna Bernard Musyokiya mai shekaru 35 a Duniya ya bayyana irin matukar kaunar da yakewa Matar sa mai suna Deborah Jan, wanda Matar tasa ta kasan ce mai shekaru 75 a Duniya kuma tana da ‘Yaya 2.
Bernard Musyokiya ya bayyana cewa: Shi da Amaryar tasa Deborah sun kusa tafiya Kasar Amurka domin su sha Soyayyar su yadda suke bukata.
Matashin mai suna Bernard Musyokiya sun hadu da Amaryar tasa ne wato Deborah a kafar sada zumun ta ta Facebook, wanda Matashin ya kasan ce dan kasar Kenya inda a lokacin suka kulla aure a tsakanin su.
Sannan kuma Matashin ya bayyana cewa: Soyayyar gaskiya yakewa Matar sa kuma ba dan kudin ta yake son ta ba, Musyoki wanda ya kasan ce dan jihar Kitui ne a Kenya ya bayyanawa jaridar TUKO.co.ke cewa, ya hadu da Deborah ne a manhajar Facebook a shekarar 2017.
Kamar yadda Musoyoki bayyana cewa.
Na bukaci mu fara kawance da ita bayan mako guda nace mata ta aure ni kuma ta amince A 2018, Musoyoki yace ya shirya zuwa Amurka don haduwa da ita amma aka hanashi biza amma bai yanke tsammani ba.
Sannan ya kara da cewa: A shekarar 2020 ya sake neman biza kuma aka sake hanashi kuma yace basu daina tattaunawa da juna ba har karshen Disamban 2020, amma sai matar ta yanke shawaran zuwa Kenya domin haduwa da shi.
Ya kara da cewa: Muna yi barci a dakuna daban-daban kuma mun yi alkawarin ba zamu yi jima’i ba har sai an daura mana aure, a ranar biyu 2 ga watan Febrairu 2021 aka daura musu aure a Sheria kuma mutane suka shaidal.
Ya ce: Yan uwansa sun yi mamaki a lokacin da yace zai auri baturiyar mai suna Deborah, Yan Najeriya sun yi tsokaci akan wannan al’amarin domin Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakin su.
Cikin wadan da suka wadan da suka yi tofa albarkacin bakin su akan wannan al’amarin sune kamar haka.
Wata Matashiye mai suna Zainab Yusuf tace: Hhhhhh to wlh Koni yadda nake Shan luguden wahala a Nigeria dana samu wacce zatayi wup Dani wallah Ina fecewa.
Hauwa’u Muhammad tace: Hmmmm… Ba dole yaso taba, ita ba dole tasoshi ba, Abar kaza cikin gashin ta kawai.
Salisu Nasir yace: Kamar na dankara ashar wallah Wai soyayya nabi soyayya da Dan banzan guda na daushi keyar ta da katako tirrrrr.