Advertising
Advertising
Labarai

Sheikh Abduljabbar yayi wata magana kafin a kai shi kurkuku akan Mukabalar da sukai da Malaman Kano

Har yanzu dai Duniya ta kasa yin shiru akan lamarin Abduljabbar da Gwamnan Kano wanda har yanzu ake ta tafka shari’a a kai.

Advertising

Wasu da dama suna ganin cewa: Ba’a yiwa Abdauljabbar adalci akan abubuwan dake faruwa ba, inda wasu kuma suke ganin ai ya cancanci abin da akai masa kuma Gwamnati tayi dai-dai da ta kulle shi a kurkuku.

To har yamzu dai wannan dambarwar tana ci gaba da hauhawa, inda kowa yake jiran yaga abin da zai faru a karshen lamarin.

Kamar yadda kuka sani shi dai Abdauljabbar ana zargin sa ne da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad S.A.W da kuma Sahabban sa, inda shi kuma kullum yake musanta wannan magana.

Advertising

Wannan kuma shi ne yada Gwamnatin Jihar Kano ta shirya zaman Mukabala tsakanin Abduljabbar din da kuma Malaman da suke kalubalantar sa, domin a sami damar ware aya daga tsakuwa.

Inda Gwamnatin ta hada zama tsakanin Abduljabbar din da wasu Malamai guda hudu 4 daga bangaten Izala, Salafiyya, Tijjaniyya da kuma Kadiriyya, sannan kuma aka dauko wanda zai zama alkali a Mukabalar wanda shima ya kasance a bangaren Izala.

Domin kuji cikekken labari akan maganar da Abdiljabbar yayi kafin a kai shi kurkuku game da Mukabalar da suka yi, sai ku kalli bidiyon da muka ajiye a kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button