Wata Budurwa ‘Yar TikTok tayi rawa da Duwawunta domin Mutanen da suke zagin ‘Yam Matan TikTok suji haushi
Kamar yadda kuka sani a wannan lokacin ‘Yam Mata da yawa suna wallafa bidiyon kan su a dandalin TikTok wanda hakan yake janyo musu zagi da munanan maganganu, domin suna abin da bai dace ba a cikin bidiyon.
Idan bazaku manta ba a ‘Yan kwanakin nan wani al’amari ya auku a dandalin TikTok kan wasu ‘Yam mata da suke tonawa kan su asiri akan wata hatsaniya daga shiga tsakanin su, inda suke wallafa bidiyon suna cin mutuncin junan su.
Sannan kuma Malamai da dana suna yawan nasiha akan ‘Yam matan da suke wallafa bidiyon su a dandalin TikTok suna abin da bai dace ba a ciki, inda har ma ake kwatan ta abin da suke da zai iya zame musu musufi nan gaba a rayuwar su.
To a yau ma mun sami wata bidiyo daga Tashar “Tsakar gida” dak kan manhajar Youtube, inda suka wallafa wata bidiyon Mata ‘Yan TikTok da wani al’amari ya shiga tsakanin su da wani Mutumi da ake masa lakabi da mai Gemu.
Sannan kuma a cikin bidiyon munga wata Matashiyar Budurwa tana bayani akan cewa, a duk lokacin data wallafa bidiyon ta a dandalin TikTok Jama’a suna mata cece-kuce da cewa tana rawa da Duwawunta tare da jujjuya kugu.
Amma cece-kucen da Jama’a suke mata akan abin da take aikatawa a dandalin TikTok din sai ma ta kara cigaba da abin da take, inda nan take ta wallafa wata bidiyo tana sake yin rawa da Duwawun nata sannan kuma tana cewa.
Duk wanda yake da abu shi yake nunawa da wanda bashi da shi ba sannan ta kara cigaba da wara da Duwawunta, wanda hakan yana nuna maganar da Jama’a suka yi akan ta sun sake kara mata azama ta cigaba da abin da take.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuga yadda wannan Budurwar take abin da bai dace ba.