Labaran Kannywood

Yadda rayuwar Jaruma Halima Atete ta kasance da kuma daukakar data samu a Masana’antar Kannywood

Kamar yadda kuka sani Jaruma Halima Yusuf wacce aka sani da Halima Atete tana daya daga cikin Ficaccun Jaruman Masana’antar Kannywood Mata wanda suka taka rawar gani sosai a Masana’antar.

To yau wannan lokacin ma Jaruma Halima Atete ta sake samin wata daukaka a Masana’antar Kannywood wanda a yanzu take kara taka rawar gani, sannan kuma tauraruwar ta take haskakawa.

Shahararran Dan Jarida wanda yake aiki a Gidan Jaridar Legi shi ne ya tattaro takaicaccan tarihin rayuwar Jarumar, da kuma taka rawar ganin da tayi a Masana’antar Kannywood inda ya wallafa a shafin sa na sada zumunta.

Ga abin daya rubuta a shafin nasa game da rashirin rayuwar Jaruma Halima Atete da kuma daukakar data samu a Masana’antar Kannywood.

Jarumar Kannywood Halima Yusuf Atete: An haifi @haleemaatete a ranar 26 ga watan Nuwambar 1988, a garin Maiduguri, jihar Borno.

A shekarar 2012 ta fara fitowa a cikin fina finan Hausa, kuma tayi fina-finai da yawa, amma fim ɗin Ƙona Gari, Asalina da Dakin Amarya su ne suka sa Atete ta shahara.

Ta fi fitowa a matsayin mace mai zafin kishi, marar mutunci ko yar bariki (a cikin fina finai), Ta fito a fina finai sama da 160, amma ga wasu kaɗan daga cikin fina finan da Atete ta fito a cikin su.

– Wata Hudu, Yaudarar Zuciya
– Asalina, Kona Gari , Ba’asi
– Dakin Amarya, Matar Jami’a
– Wata Rayuwa, Ashabul Kahfi
– Maidalilin Aure , Mu’amalat
– Soyayya Da Shakuwa , Igiyar Zato
– Alkalin Kauye, Bani Bake
– Kurman Kallo, Uwar Gulma
– Bikin ƴar gata, Alƙalin ƙauye,Labarina.

74 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button