Advertising
Advertising
Labarai

Duk ‘Yan Arewa munafukai ne sunyi shiru basa iya magana sabida dan Arewa ne yake mulki to ba’a fara shan wahala ba har yanzu, cewar Ai’sha Yesufu

Ai’sha Yesufu tayiwa Al’ummar dake Arewacin Nageriya zazzafan martani inda ta hada tare da mutanen da suke mata tsokaci a karkashin wallafar da tayi, kamar yadda take fadin cewa yawancin ‘Yan Arewa basu da abin yi sai lokacin zabe yazo a dauke su kamar awaki domin ku kada Kuri’a.

Advertising

Ai’sha Yesufu ta kara da cewa: Bata ga amfanin shugabancin Kasar dan Arewa ba inda ta kara da cewa, za’a yi bayani da kyau domin duk wani dan Arewa yaji da kunnen sa da kyau sannan kuma ya fashim ta.

Kamar yadda Jaridar Labarunhauda ta ruwaito cewa: Ai’sha Yesufu ta tace rashin tsaro ne yake lalata yankin Arewacin Nageriya amma sabida munafinci irin na ‘Yan Arewa, baza su bude baki suyi magana ba sabida dan Arewa ne yake shugabanci.

Ai’sha Yesufu ta kara da cewa: A lokacin da Goodluck Ebele Jonathan yake kan mulki babu wani dan Arewa da yasan kaddara.

Advertising

Wanda a lokacin ne Malamai da masallatai suka dinga fitowa suna maganganu tare da cece-kuce sannan kuma tace duk wata tsiya daga Arewa take fitowa, ta kara da cewa talauci ya yiwa ‘Yan Arewa katutu sannan kowa yasan yadda Kasar Nageriya take fama da fatara.

Inda tace: Satar Mutane a Kasar Nageriya yafi satar Akuya sauki, inda tace hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama bala’i ana satar Mutane kamar da gangan.

Ai’sha Yesufu ta kara da cewa: Al’umma sun yi shiru da sunan addu’a suke ba tare da suna yin magana ba, kuma basa yiwa shugaban Kasa bayanin komai inda tace ba’a fara shan wahala ba a Kasar nan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button