Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Jamila Nagudu tare da babban Dan ta Mus’ab sun wallafa wata bidiyo da Jama’a suka yi farin ciki da su a lokacin da suka je aikin Umara Saudia

Ficacciyar Jarumar Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood Jamila Umar Nagudu wacce aka fi sanin ta da Jamila Nagudu, tana daya daga cikin Jaruman Masana’antar Kannywood wanda suka yi tashe a shekarun baya sannan suka taka rawar gani sosai.

Advertising

Kamar yadda wasu daga cikin ku suka sani Jaruma Jamila Nagudu tana da wani matashin Saurayin Dan ta wanda zai kai shekara goma sha takwas, wanda shi ne babba Dan ta na farko.

To a yau ne muka sami wata bidiyon wanda Tahsar Tsakar gida ta wallafa inda mukaga Jaruma Jamila Nagudu tare da wannnan matashin Dan nata mai Mus’ab sun dauki bidiyo a lokacin da suke Umarar tare.

Jaruma Jamila Umar Nagudu tare da Dan nata Mus’ab sun dauki wannan bidiyon ne cikin farin ciki da godiyar Allah, da ya kawo su wannan lokacin da har suka sami damar zuwa aikin Umara tare, Kamar yadda zaku bidiyon nasu a kasa.

Advertising

Jaruma Jamila Nagudu ita ma a yanzu ta zama babbar Uwa domin gashi a yanzu Dan ta na farko ya zama babba wanda za’a sa shi a layin samari masu tasowa, wanda zuwa nan da wasu shekaru za’ana iya zata masa aure.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kuga yadda Jaruma Jamila Nagudu tare da Dan nata Mus’ab suka dauki bidiyon nasu cikin farin ciki da murna a lokacin da suka tafi aikin Umara tare.

Kalli bidiyon dake kasa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button