Jarumar shirin Kwana casa’in Rahama MK Matar Bawa Maikada tayi aure cikin sirri daba kowa ne ya sani ba
Kamar yadda kuka sani Rahama MK Ficacciyar Jaruma ce a cikin shirin nan mai dogon zango wato Kwana casa’in wanda Tashar Arewa24 take haskawa, wanda a yanzu ba’a ganin Jarumar a cikin shirin na Kwana casa’in.
A lokacinda masu kallon shirin Kwana casa’in suke son ganin ya zata kaya da Matar Bawa maikada wato Rahama MK, sai kuma gashi tayi Auren ra cikin sirri ba tare da wasu sauran Al’umma sun sani ba.
An daura Auren Jaruma Rahama MK da Angon nata a gidan su dake birnin Jihar Kano cikin wanu yanai daba kowa ne ya sani ba, inda aka yi komai da komai aka gama cikin sirri.
Dama Jaruma Rahama MK ta jima tana bukatar yin aure amma bata bayyana domin Jama’a su sani ba, kwatsam sai ji aka yi tayi Auren ta ba tare da sanin kowa ba.
Wakilin Jarudar Damukaradiyya ya bukaci jin ta bakin Jaruma Rahama MK a wayar salula inda Jarumar ta tabbatar masa da wannan maganar, tana mai ce masa.
Dama kamar yadda na fada maka bayan kwana uku 3 da suka gabata zan yi Aure a wannan ranar kuma gashi Allah ya cikamin burina, kuma fatan da nake da shi Allah ya sa na sami haihuwa kuma na mutu a dakin Mijina.
Game da harkar Fim Jaruma Rahama MK ta bayyaan cewa: Zata cigaba da fitowa a cikin shirin Kwana cada’in sai dai kuma sauran Fina-Finai ne babu tabbas ta fito a ciki.