Masha Allah: An daura Auren Jaruma Laila ta shirin Labarina shi yasa aka daina ganin ta a cikin shirin
Kamar yadda kuka sani Maryan Wazeery waccr aka fi sanjn ta da Laila ta cikin shirin Labarina mai dogon zango, tajima sosai ba’a ganinta a cikin shirin na Labarina inda Jama’a suke tunan ko huku ta tafi.
To a yau kuma mun sami wani labari mai dadi akan Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina wanda a dalilin hakan ta daina fitowa a cikin shirin Labarina.
Ficaccan Daraktan Masana’antar Kannywood Malam Aminu Saira wanda shine ya shirya wannan shirin Fim din na Labarina, shi ne ya wallafa labarin abin da yada aka daina ganin Jaruma Laila a cikin shirin Labarina.
Ga wallafar da yayi kamar haka.
A madadina da Kamfanin Saira Movies Tv muna taya ‘Yar uwa Maryam Wazeery murnar Auren da tayi a yau, Allah ya basu zaman lafiya Allah kuma ya basu zuriya dayyiba, congratulation muna missing din ki Laila.
Wannan wallafar da Ficaccan Darakta Malam Aminu Saira yayi a shafin sa na sada zumunta Instagram yana nuna cewa, Auren Jaruma Laila aka yi shi yasa ba lallai bane a cigaba da ganin ta a cikin shirin Labarina mai dogon zango.