Labaran Kannywood

Kalli Hotunan Auren Jaruma Laila ta shirin Labarina tare da Angon ta Tijjani Badamasi Dan Kungiyar kwallon Kafa Super Eagles

Kamar yadda kuka sani a jiya Juma’a ne aka daura Auren Ficacciyar Jarumar Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood, Maryam Wazeery wacce ake kiran ta da Laila a cikin shirin Labarina mai dogon zango.

An daura Auren Jaruma Laila da shahararran Dan wasan Kwallon Kafa na Kasar Nageriya “Super Eagles” wato Tijjani Badamasi.

A jiya labarin Auren Jaruma Laila ta shirin Labarina yayi ta yawo a kafafan sada zumunta inda Jama’a da dama suke mamakin wannan labarin, domin Auren nata ne yazowa da Mutane bazata ba kamar yadda aka saba yin Auren Jaruman Kannywood ba.

Ga hotunan Jaruma Laila nan tare da Angon nata wato Tijjani Badamasi wanda yake shahararran Dan wasan Kwallon Kafa na Nageriya “Super Eagles”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button