Advertising
Advertising
Labarai

Wata Yarinya mai suna Aisha Dalil ‘Yar shekara 18 tayi nasarar lashe gasar rubutu da aka na BBC Hausa a wannan shekarar

Wata matashiyar yarinya mai suna Aisha Dalil tayi nasarar lashe gasar da aka yi mai suna Hikaya ta wanda BBC Hausa take shiryawa a duk shekara.

Advertising

Aisha Dalil tayi nasarar lashe gasar da aka yi ta wannan shekarar da muke ciki inda ta rubuta wani labari mai taken “Hakkina”.

Idan baku manta ba a jiya Juma’a ne da daddare aka bayyana cewa, Aisha Dalil tayi nasarar lashe wannan inda tazo a matsayin ta daya 1 a bikin kammala gasar da aka yi a Abuja.

Aisha Dalil ta sami babbar kyautar kudin Amurka kimanin Dala dubu biyu $2000, sannan kuma aka bata lambar girmamawa akan nasarar da ta samu a gasar wannan shekarar da aka yi.

Advertising

Aicha Abdoulaye mai shekara 27 ‘Yar ƙasar Nijer ita ce ta zo ta biyu a gasar inda a ka bata kyautar kuɗi, Dalar Amurka dubu daya $1,000 da lambar girma bayan ta rubuta labari mai taken “Butulci.

Zullaihat Alhassan ce ta zo ta uku da labarin da ta rubuta mai taken “Ramat”, wanda ke magana a kan haƙƙin masu ƙaramin ƙarfi, inda ta samu Dala dari biyar $500 da lambar girma.

A jawabin da ya yi a taron, Shugaban sashen BBC a Nijeriya, Aliyu Tanko ya ce a bana an samu wadanda su ka shiga gasar daga Kamaru, Sudan, Jamhuriyar Nijer da sauran ƙasashen Afirka.

Sannan yace: yana fatan labarin da ya lashe gasar ta bana zai zamto maganin matsalolin da ke damun al’umma.

Bayan ya taya waɗanda su ka lashe gasar, Tanko ya kuma haƙurƙurtar da waɗanda ba su samu nasara ba, inda ya ce “ina fatan a baɗi ku ne za ku samu nasarar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button