Advertising
Advertising
Labarai

Dakatar da Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari daga aiki ba komai bane illa cin amanar tsaron Nigeria, daga Datti Dattifi

Daga Datti Dattifi.

Advertising

Dakatar da Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari daga aiki ba komai bane illa cin amanar tsaron Nigeria, ku ganshi a 2019 yana sanar da cewa ya koma kan hanyar Kaduna zuwa Abuja wanda a yanzu hanyar ta koma tarkon
mutuwa.

Imbanda cewa Gwamnatin shugaba Buhari ta zama tamkar sokuwar Gwamnati ya za’ayi ku bude kofar da za’a dakatar da wannan mutumi saboda kawai wakilan IPOB sun kitsa sharri sannan ku amince a dakatar
dashi?.

Da wahala kaga babban ofisa a rundinar soji ko Police wanda ya kai matakin matsayi irin na Abba Kyari yana jan ragamar mayaka domin fafatawa da ‘yan ta’adda.

Advertising

Ya hakura da zaman ofishin da sanyin AC ya fito bakin daga da kansa, ya sadaukar da rayuwar sa da lokacin sa da jin dadin sa amma ku rasa abinda zaku saka masa dashi sai wulakanci da tozarci.

Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari don girman Allah ka yiwa mutanen can magana su dawo da Abba Kyari. Allah Ka isar mana

Mun sami wannan labarin ne daga shafin “Rariya Hausa” dake kan kafar sada zumunta fa Facebook.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button