Advertising
Advertising
Labarai

Duk fadin Kasar Nageriya babu wanda ya kai Shugaba Muhammad Buhari Gaskiya, cewar Mawaki Dauda Kahutu Rarara

Daga: Fahad Kabir Mai Tata.

Advertising

Shahararran Mawakin Siyasar Kadar Nageriya Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa, bau ga wani Mutum da yafi shugaban Kasa Muhammad Buhari gaskiya a Kasar Nageriya ba.

Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bayyana hakan ne a lokacin da suke zantawa da manema labarai a Jihar Kano, sannan ya kara da cewa.

A fannin shugaba Muhammad Buhati ko Gwamnan su na Jihar Katsina Masari baya fadin wani abu na san rai, gakiya zallarta yake fada a kan su.

Advertising

Rarara ya kara da cewa: Sau da yawa ina duba Jama’ar da suke sauraron Waka ta ne idan zan rubuta ba wai na kalli su da zan yiwa wakar ba.

Sannan kuma Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa: Dalilin da yasa yafi yiwa Gwamna Masari da shugaba Muhammad Buhari waka shi ne, bai ga wanda ya kai shugaba Muhammad Buhari gaskiya ba a Nageriya.

Sannan kuma bai ga wanda ya kai Gwamna Masari iya Siyasa ba a Jihar Katsina, sannan kuma yace maganar cece-kuce da Jama’a suke ai dama bazaka hana Jariri kuka na idan har baza ka ba shi abinci ba.

Domin an kwashe tsawon shekaru goma sha shida 16 ana barna a Kasar Nageriya ga rashin kudi ga annobar Korona, duk inda aka kalla sun taimaka wajan tsintar kai a halin da aka shiga yanzu ba wai shugaban Kasa ba ne.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button