Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa nan da ranar Talata mai zuwa za’a bude layukan Wayar Salula domin a cigaba da yin Waya

Kamar yadda kuka sani a Jihar Zamfara da wasu yankuwan an hana amfani da layukan Wayar salula domin wasu matsaloli da ake samu ta dalilin hanyar sadarwa.
A yau kuma Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya bayyana cewa, nan da ranat Talata mai zuwa za’a bude layukan Wayar salula a duk fadin Jihar.
Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da ake zaben Shuwagabannin Jam’iyar APC rehen Jihar Zamfara, a ranar Asabat data gabata.
A farkon wannan Watan da muke ciki ne aka dakatar da yin amfani da layukan Wayar salula domin dakile hare-haren da ‘Yan Bindiga masu garkuwa da Mutame suke kai wa.
Sai dai a kwanakin baya Gwamnatin ta bada umarnin bude layukan Wayar salular domin a cigaba da yin amfami a yanar gizo-gizo, wanda hakan ya faru ne a Gusau babban Birnin Jihar ta Zamfara, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Sannan kuma Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya kara da cewa: Za’a bude kasuwannin da aka rufe sabida matsalar tsaro.
Gwamnan ya kara da cewa: Wandan nan labaran da suka bayyana suna nuna cewa, da alamu an fara samin raguwar matsalolin tsaro a fadin yankunan Jihar ta Zamfara, sannan kuma nan da ranar Talata za’a sake bude layukan Wayar salula domin kowa da kowa ya sami damar yin Waya.