Advertising
Advertising
Labarai

Izgiline ga duk wanda yake sanya kida yana yabon Manzon Allah S.A.W, cewar Sheikh Bello Yabo Sokoto

Shahararran Malamin addini Sheikh Bello yabo dake Jibar Sokoto a wani Karatu daya gabatar yayi magana akan masu kida suna Yabon Manzon Allah S.A.W.

Advertising

A cikin karatun nasa Sheikh Bello Yabo ya bayyana cewa: Yawan zinace-zinace da ake a wannan zamani da kuma kide-kide alama ce ta tashin Alkiyama.

Sannan kuma yake cewa: A yanzu idan za’a yi yabon Manzon Allah S.A.W sai an sanya kida a ciki, wanda yace kada a yi amma don zakayi yabon sa sai ka sanya kida inda yace ai kwanda na Shata da naka.

Sabida wannan kidan daka sanya a lokacin da zaka yi yabon Manzon Allah S.A.W izgilanci kayi.

Advertising

A cikin bidiyon da Sheikh Bello Yabo yake karatun nasa zakuji yadda yake bayani sosai akan masu yabon Manzon Allah S.A.W sannan kuma su sanya kida a ciki.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button