Advertising
Advertising
Labarai

Sheikh Nuru Khalid ya sami sabon Masallacin da zai cigaba da Limanci

Sheikh Nuru Khalid ya sami sabon Masallacin da zai cigaba da Limanci

Bayan awanni da kwamitin Masallacin Juma’a na Apo ya sanar da sallamar shi gaba daya, Sheikh Nuru Khalid ya samu wani Masallacin da zai cigabs da limanci.

Advertising

Wannan na zuwa ne a ranar da Kwamitin Masallacin na Apo ya sanar da sallamar shi gaba daya, bayan ya dakatar da shi tun da farko.

A karshen makon nan ne dai Kwamitin Masallacin karkashin Sanata Sa’idu Dansadau ta fitar da sanarwar dakatar da Malamin daga limancin sabida hudubarsa ta ranar Juma’a a kan matsalar tsaro.

To sai dai kuma jaridar Aminiya ta rawaito cewa, Sheikh Nuru yace tuni Kwamitin Gudanarwar sabon Masallacin Juma’ar da aka gina a unguwar ma’aikatan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ba shi limanci a can.

Advertising

Yace, zai fara jagorantar sallah ne daga ranar
Juma’a, takwas ga watan Afrilun 2022 mai zuwa.

Ya ce, da yardar Allah zan fara jan sallah a sabon masallacina ranar Juma’ar nan mai zuwa sabida a matsayinmu na limamai, dole sai mutum ya samu wajen da zai rika limanci.

Akwai sabon masallacin da muka gina a bayan unguwar CBN, ni ne zan rika jan sallaha can, inji shi.

Malamin dai ya bayyana sallamar da aka yi masa daga masallacin na Apo a matsayin
kaddararsa, sabida ya fadi gaskiya.

A yayin hudubar tasa dai, Malamin ya kalubalanci gwamnati mai ci kan yadda yace ta gaza magance matsalar tsaron da ya addabi al’umma, musamman ma a kan harin jirgin kasan da aka kai a tsakanin Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button