Jami’an tsaro sun yi nasarar hallaka wani gawurcaccan dan Bindiga mai suna Yellow Magaji Arushe
A yau ne muka sami labarin abin farin ciki yadda Jami’an tsaro sukayi nasarar hallaka wani shahararran dan ta’adda wato dan Bindiga ma suna, Yellow Magani Arushe.
Wanda Ficaccan Jarumi sannan kuma Darakta mai bada Umarni a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood wato “Falalu a Dorayi” shi ne ya wallafa wannan labarin kamar yadda yake cewa.
Jami’an Yansanda sun yi dirar mikiya Sun harbe YELLOW MAGAJI (ARUSHE)
wani dan bindiga da ya yi kaurin suna a hanyar Kaduna-Abuja.
A wani hotel da Yan ta’addan ke kwana mai suna SIR JOE GUEST INN, da ke No. 8 titin Sajo, Unguwan Maigero Sabon Tasha, karamar hukumar Chikun jihar Kaduna.
Sannan kuma Jami’an tsaron sun yi nasarar kwacewa makamai da kuma abubuwa hawa a wajan ‘Yam Bindigar, muna rokon Allah ya kara bawa Jami’an tsaro kwarin Gwiwa da yin nasara akan ‘Yan ta’addan da suke addabar kasar mu ta Nageriya, Ameen.
Ga hotunan ‘Yan Bindigar nan wanda Jami’an tsaro suka hallaka shi sai ku kalla.