Jarumar shirin Labarina Laila ta bayyana wani sirri game da Kamfanin Saira Movies daba kowa ne ya sani ba
Kamar yadda kuka sani a ranar Juma’a ne aka daura Auren Jarumar shirin Labarina mai dogon zango wato Maryam Wazerry wanda ake mata lakabi da Laila a cikin shirin Labarina.
Ficaccan Darakan shirin Labarina Malam Aminu Saira ya wallafa labarin Auren Laila wacce Jaruma ce a cikin shirin Fim din nasa a shafin sa na sada zumunta Instagram a ranar Juama’a.
Inda ya wallafa rubutun nasa kamar haka: A madadina da Kamfanin sairamovies Muna taya “Yar uwa maryam wazeery Murnar Auren da tayi a yau. Allah ya basu zaman Lafiya, Allah kuma ya basu zuriya dayyiba congratulations muna missing din ki LAILA Labarina Inji shi Malam Aminu saira.
Bayan Darakta Aminu Saira ya wallafa labarin Auren nata nan take Jaruma Laila take kasan labarin inda ake tsokaci wato Comment a turance, tana Mai Cewa ameen ya hayyu ya qayyum nagode sosai, bazan manta da saira movie ba Inji Jaruma Maryam Wazeery Laila.
Jarumar ‘yar Asalin jihar Gombe an daura Auren ta a Ranar juma’ar data gabata a mahaifarta dake kaltingo ta Jihar Gombe anyi wannan aure ne Babu zato Babu tsammani cikin sirri.
Jaruma Maryam Wazeery ta sami wannan daukakar ne tun farkon bayyanar ta a cikin shirin Labarina mai dogon zango, wanda Ficaccan Darkta Malam Aminu Saira ya shirya shi.