‘Yan Kato da Gora sun yi Nasarar hallaka wasu ‘Yan Ta’adda guda 3 sannan suka kama daya da ran sa a lokacin da suka kai hari ga wasu Manoma
Jami’an ‘Yan Kato da Gora wanda suke taimakawa Sojoji wajan kama ‘Yan ta’addan Arewacin Nageriya sun yi nasarar kama wani dan ta’adda guda daya, sannan kuma su hallaka wasu ‘Yan ta’addan guda uku.
‘Yan Kato da Gorar suna hallaka wadan nan ‘Yan ta’addan ne a lokacin da suke satar amfanin Gonar da wasu Mutane suka noma, a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Kamar yadda Jaridar PR Nigeria ta ruwaito cewa: ‘Yan Kato da Gorar sun yaki ‘Yan ta’addar ne a lokacin da suka kaiwa wasu Manoma hari, sannan kuma suka sace musu amfanin Gonar tasu.
Wata majiya ta shaidawa PR Nigeria cewa: A ranar Alhamis da misalin karfe uku 3:30 na yamma ‘Yan ta’addan suka kaiwa Manoman hari a kusa sa Kauyen Daiwa.
Majiyar ta kata da cewa: ‘Yan ta’addan sun kashe Manoma guda biyu 2 ta hanyar harbin su sannan kuma suma raunata wani Manomi guda daya 1.
Nan take ‘Yan Kato da Gora din wanda suke ƙarƙashin jagorancin kwamandan sashin binciken sirri na CJTF, Saminu Audu su ka datsi ‘Yan ta’addan a Lamboa, tsakanin Minok-Janaka a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Bayan sun fafa yaki da ‘Yan ta’addan sun yi nasarar hallaka guda uku 3 sannan kuma suka kama guda daya 1 da ran sa.
Wanda ‘Yan ta’addan ire-iren sauran yaran Abubakar Shekau ne da su ka ƙi yin mubaya’a ga ISWAP, sun dogara ne da garkuwa da mutane da kuma fashi domin su sami abin da za su ci.