Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Duk Masana’antar Kannywood bani da Uban Gida idan kuma akwai wanda ya koyamin Fim yayi magana, cewar Sulaiman Bosho

Ficaccan Jarumin Masana’antar Kannywood Sule Yahaya Hamma wanda kowa yafi sanin sa da Sulaiman Basho ya ya bayyana wani al’amari da Jama’a suka yi mamakin abin da ya fada.

Advertising

Jarumi Sulaiman Bosho yake cewa: A duk Masana’antar Kannywood ba shi da wani Uban gida wanda zai ce shi ya kowar da shi harkar Fim Masana’antar.

Sulaiman Bosho ya bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da Gidan Jaridar Damukaradiyya, inda a lokacin yake fadin cewa.

Wannan harkar Fim din ta Masana’antar Kannywood da shi aka fara ta wanda a yanzu haka an dauki tsawon shekaru talatin 30, don haka bani da Uban Gida a Masana’antar Kannywood.

Advertising

Sannan ya kara da cewa: Idan kuma akwai wanda ya koya mini ya futo ya fada, amma dai ni nasan bani da Uman Gida a Masana’antar shirya Fina-Finai ta Kannywood domin ina cikin ta ne tun farkon kafuwar ta.

Bayan haka ya bayyana wani burin sa da yake son cika shi game da harkar tasu ta Fim, inda yake cewa.

 A gaskiya buri na shi ne mu yi amfani da fim wajen isar da kyawawan dabi’u na Musluci da Kuma al’adun mu a duniya, don haka ina alfahari da harkar saboda sana’a ta ce wadda ta rufa mini asirin.

Sannan ya kara da cewa: Don mun samu arziki a cikin ta na yi aure na yi motoci Kuma da ita mu ke ciyar da iyalan mu har ma mu ke yi wa mutane alheri da abun arzikin da mu ke samu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button