Advertising
Advertising
Labarai

Kotu ta Umarci Gwamnan Jihar Kano Ganduje daya biya Sunusi Lamido Sunusi tarar Naira Miliyan 10

Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta yanke hukunci akan korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga Jihar Kano bayan tsige shi da aka yi daga kan Mulkin Sarauta.

Advertising

Mai shari’a Anwuli Chikere ya yanke hukuncin inda yake cewa: Dokar da gwamnatin Jihar Kano ta yi amfani da shi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa, Alkalin kotun ya ce duk wata doka da ta ci karo da na kasa watsi da ita ake yi ya kuma umurci gwamnatin ta biya Sanusi II diyyar N10m

A ranar Talata ne wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci akan cewa korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga Jihar Kano ya sabawa doka da kudin tsarin mulki, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mai shari’a Anwuli Chikere, cikin hukuncin ya jadadda cewa: Dokar Masarauta ta 2019 da gwamnatin Jihar ta yi amfani da shi wurin korar Sanusi ta ci karo da kudin tsarin mulkin Nigeria ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Advertising

A cewar Chikere: Kundin tsarin mulkin Nigeria yafi kowanne doka karfi don haka duk dokar ta ci karo da ita za a yi watsi da ita ne, The Nation ta ruwaito. Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa.

Mr Sanusi wanda aka tsige a ranar 9 ga watan Maris din 2020 ya yi karar Sufeta Janar na yan sanda da shugaban SSS, a ranar 12 ga watan Disambar 2020 kan ‘tsare shi ba bisa ka’ida ba.

A karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/357/2020, ya kuma yi karar Antoni Janar na Jihar Kano da Antoni Janar na kasa.

Sanusi bai kallubalanci tsige shi ba duk da cewa Mr Sanusi ba ya kallubalanta tsige shi da aka yi ba, ya shigar da kara kotu inda a tabbatar masa da damarsa na zuwa duk inda ya ke so.

Sannan Ya kallubalanci wadanda ya yi karar saboda cin fuska da keta masa hakkin sa na dan adam, mai Shari’a Chikere wanda ya cire sunan Antoni Janar na kasa daga karar, ya bukaci sauran wadanda aka yi karar su dena cin mutuncin Sanusi.

Kotun ta kara da cewa: A biya Sarki Sanusi II diyyar N10m, Har wa yau kotun ta umurci wadanda aka yi karar su biya Sarki Sanusi II diyyar Naira miliyan 10 sannan su nemi afuwar sa a wallafa a manyan Gidajen Jaridu na kasa guda biyu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button