Labarai

Wani Bafulatani yayi alkawarin sai ya kashe kan sa matukar bai sami ganin Mawaki Nuran M Inuwa ba

Soyayya gamon jini inji Bahaushe: Wani bawan Allah wanda da alamu Bafulatani ne wanda ya kasan ce Masoyin Ficaccan Mawaki Nura M Inuwa, yayi alkawarin zai kashe kan sa matukar Mawakin bai cika masa burin sa ba.

Kusan dai zamu iya cewa wannan ba sabon abu bane wato yadda Jarumai da Mawaka suke haduwa da Masoyan su a gurare da daban-daban.

Mawaki Nura M Inuwa dai ya hadu da wannan Masoyin nasa ne akan hanya, kamar yadda zaku gani da idon a cikin bidiyon dake kasa.

wanda a cikin bidiyon ake tambayar Bafulatanin cewar mai yake so inda yake bayyana cewa shi Mawaki Nura M Inuwa yake so, sannan kuma yake fadin cewa idan har bai sami damar magana da Mawaki Nura M Inuwa ba zai iya rasa rayuwar sa.

Sannan a cikin bidiyon zaku ji yadda Bafulatanin yake cewa a baya yana da Aure amma ta sanadin bai sami ganin Mawaki Nura M Inuwa ba ya kashe Auren nasa.

Domin kuji abubuwan da Bafulatanin yake fada akan bai sami ganin Mawaki Nura M Inuwa ba, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button