Advertising
Advertising
Labarai

Wata Kotun tarayya dake Abuja ta rushe Zaben Jam’iyyar APC na Abdullahi Abbas a Jihar Kano

Wata kotun ta rayya dake Abuja wanda take karkashin jagorancin Hamza Muazu ta rushe zaben Shugabancin Jam’iyyar APC, da kuma tsagin Gwamnatin Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Advertising

Sannan kuma mai shari’ar ta tabbatar da Zaben da kuma tsagin tsohon Gwamnan Jihar Kano Ibrashim Shekarau wanda ya gudanar.

Kamar yadda Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa: mai shari’ar yace zaben na bangaren Ibrashim Shekarau wanda Haruna Danzago ya lashe, yasa mun sanya hannun mutum 7 daga cikin wadanda uwar jam’iyyar ta turo jihar Kano domin gudanar da zaben.

Mai shari’a Hamza Muazu wanda shine Alkalin Kotun yace ya amince da zaben da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar.

Advertising

Sannan kuma Alkalin ya yanke hukuncin cewa: bangaren Shekarau mai taken G-7 ya gudanar da zaben wanda kwamitin mutane 7 na APC ya sanya wa hannu.

Haka kuma Jaridar ta ruwaito cewa: wadanda suka shigar da kara sun hada da Muntaka Bala Sulaiman da mambobin jam’iyyar 17,980, yayin da wadanda ake karar su ne APC.

A matsayin wanda ake kara na daya, Mai Mala Buni wanda shine shugaban rio, Sen. John Akpanudoedehe sakataren jam’iyyar na kasa da kuma Hukumar Zabe ta Ƙasa, INEC.

Sannan kuma Kotun ta bayyana cewa: Duk taron da bangaren Ibrahim Shekarau ya jagoranta sahihine, Nuraini Jimoh, SAN shi ne lauyan Masu Kara yayin da Sule Usman, SAN, M.N. Duru da Mashood Alabelewe Suka kasance Lauyoyin Waɗanda ake Kara.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button