Masha Allah: Jaruma Ummi Rahab ta sami yabo kan wasu zafafan Hotunan data wallafa da suka dauki hankulan Jama’a da dama
Kamar yadda kuka sani Ummi Rahab Ficacciyar Jaruma ce a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood wanda a yanzu take kan sharafin ta, wanda Jarumi Adam a Zango ya reneta tun tana karamar yarinya har kawo wannan lokacin data girma.
Ummi Rahab ta fara bayyana ne a cikin shirin Kin Zamo Takwara Ummi wanda Jarumi Adam a Zango ya fito a matsayin Mahaifinta Jaruma Jamila Nagudu ta fito a Matsayin Mahaifiyar ta, wanda tun lokacin ta fara samin daukaka.
Sannan kuma a lokacin data girma wato yanzu Jaruma Ummi Rahab ta sake bayyana a cikin wani shirin Fim mai suna “Farin Wata Sha Kallo” wanda Ficaccan Jarumin Kannywood ya shirya shi wato Adam a Zango.
Inda Jarumar ta sake samin daukaka a tauraruwar ta ta sake haskakawa a cikin shirin wanda a yanzu haka Jaruma Ummi Rahab tana da tarin masoya masu yawa, wanda har ma ake kwatanta ita ce Jarumar da tafi yawan masoya a wannan lokacin.
To a yau kuma mun sami wasu zafafan Hotunan Jaruma Ummi Rahab wanda ta wallafa su a shafin ta na sada zumunta Instagram, inda Hotunan nata suka dauki hankulan Jama’a da dama kamar yadda dama ta saba wallafa Hotunan da suke daukar hankulan Jama’a.
Ga Zafafan Hotunan Jaruma Ummi Rahab nan a kasa domin ku kalla.