Advertising
Advertising
Labarai

Masu garkuwa da Mutane sun saki Ma’aikatan karamar Hukumar Zaria bayan an biya su Miliyan 40 Kudin fansa

Masu garkuwa da mutane sun saki ma’aikatan karamar hukumar Zariya bayan an biya su miliyan 40 kudin fansa, sannan kuma sun rike mutum 3 sai an kai musu babura.

Advertising

Rundunar yan sanda ta Jihar Kaduna ta tabbatar da sakin Mutane 10 da ga cikin 13 na ma’aikatan karamar hukumar Zariya da ke Kaduna.

Mohammed Jalige Kakakin rundunar shine ya shaidawa manema labarai a Zariya a ranar Lahadi, inda yace tun a ranar Asabar a ka sake su kuma an cigaba da kokarin sakin sauran ma’aikata guda uku.

Sai dai kuma Jalige mai mukamin ASP ya ki ya fadi ko an biya kudin fansa kafin sakin ma’aikatan, amma kuma wata majiya ta nemi a sakaya sunan ta inda ta shaidawa Kamfanin dillancin Labarai NAN cewa, ma’aikatan sai da su ka biya naira miliyan 40 sannan a ka sako su.

Advertising

Majiyar ta kara da cewa yan uwan wadan da a ka yi garkuwa da su din nen su ka hada kudaden.

Ta kara da cewa: kuma masu garkuwa da mutanen ba su saki sauran mutum uku ba sabida sharuddan da suka gindaya bayan an biya miliyan 40, shine cewa zasu rike mutum uku har sai an sai musu baburura guda uku sabbi fil.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button