Advertising
Advertising
Labarai

Ya kamata duk wani dan Nageriya ya mallaki Bindiga sabida ‘Yan ta’adda domin Shuwagabannin kasar nan bata mu suke ba, cewar Sheikh Bello Yabo

Sheikh Bello Yabo dake Jihar Sokoto yayi wani Wa’azi mai ratsa zuciya wanda Jama’a suka dinga maganganu da cece-kuce a kai.

Advertising

A cikin wata bidiyo wanda Tashar Al-Annur Media Tv dake kan manhajar Youtube ta wallafa Sheikh Bello Yabo ya baiwa Al’ummar dake Kasar Nageriya shawara akan cewa, su fara mallakar bindiga.

Kamar yadda Malamin yake cewa: Yadda harkar tsaro ta lalace a Kasar Nageriya ya kamara kowanne dan Nageriya ya nemi duk inda masu sai da Bindiga suke domin ya saya.

Sheikh Bello Yabo yake cewa:

Advertising

Mun gano cewa manyan kasar nan ba ta tamu suke yi ba suna yawo da jami’an tsaro yayin da suke barinmu hakanan.

Sannan ya kara da cewa: Duk manyan Kasar nan suna da masu tsaron lafiyar su a Gidajen su kamar ‘Yan Sanda ko Sonoji.

Bayan nan Sheikh Bello Yabo ya bayyana yadda ya ga motar wani gwamna wanda motoci biyar 5 ne a gabansa, yayin da wasu biyar 5 suke bayansa duk don tsaron lafiyarsa sabida rayuwar sa na da muhimmanci.

Malamin yace: Tunda mu ba mu da masu kula da lafiyarmu ya kamata mu dage mu nema wa kawunanmu mafita ta hanyar addu’o’i da kuma neman makamai.

Sheikh Bello Yabo ya kara da cewa: Matukar ‘Yan Bindiga suka gano kowa a shirye yake ba za su taba kai hari ba, hatta Sojoji ma kwanton bauna ‘yan bindiga suke yi musu don sai sun tabbatar su na bacci suke kai musu hari.

Ya kara da cewa: Idan abu ya kai abu har Dajuka za’a dinga bin Yan Bindiga ana kai musu hari sannan ya kara da cewa, duk wanda baya da bindiga ya tanadi Bakar sa wacce zai iya dana wa dan ta’adda a idonsa ya fashe.

Domin kuji cikekken bayani daga bakin Sheikh Bello Yabo sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

https://youtu.be/OZ0bSqW7AlU

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button