Advertising
Advertising
Labarai

Cikin fushi sabuwar Jaruma Sumayya Galadi ta aikawa da Muhammad Lawan Gusau martani akan batun daya fada a kan ta

Ba tare da bata lokaci ba Jaruma Sumayya Galadi tayi zazzafan martani ga Muhammad Lawal Gusau kan hanata Fim.

Advertising

Idan baku manta ba an wallafa wani labarin cewa: Muhamnad Lawan Gusau ya aika da wata budaddiyar wasika zuwa ga wata jaruma mai tasowa a Masana’antar Kannywood mai suna Sumayya Galadi, inda Lawan Gusau yake umartar ta da ita da wadan da suka sayyata a Fim da su gaggauta cire ta.

Sannan kuma ya Lawan Gusau ya kara umartar ta da cewa: Ta daina amfanj da kafar sadarwa ta TikTok sannan yace, wannan zubar da martabar Jihar Zamfara ne da yankin Sokoto da Kebbi daular Usmanu bin Fodio.

A cikin wakisar dai Muhammad Lawan Gusau ya bayyanan cewa: Sumayya ‘Yar wani babban Mutum ce wanda ake girmamawa a yankin, wanda ya kasance tsohon dan Majalistar wakilai maj wakiltar mazabar Shinkafi, inda Sumayya ta shi masana’antar ba tare da sanin sa ba.

Advertising

Sannan kuma yayi korafin cewa: Sumayya tayi karatun fannin kiwon lafiya da yake fatan karatun da tayi ya amfani ‘yan yankin amma tazo tazo ta bige da TikTok, inda ya basu awa 74 domin suyi gaggawar dakatar da ita ta daina Fim sannan ita kuma ta daina TikTok ko ya dauki mataki a madadin Jihohin da ya ambata yana wakilta.

Sai dai a safiyar yau da tare da bari ya huce ba Sumayya tayi sakon wani bidiyo inda ta wallafa a shafin na TikTok da kuma Instagram na martani ga Muhammad Lawan Gusau kan wannan batu, dama an ce bawa da bakin sa dai wuyar shaidawa ne da shi.

Domin kuji martanin da Sumayya ta aikawa da Muhammad Lawan Gusau a cikin wannan bidiyon da ta wallafa a shafin ta na TikTok da Instagram, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button