Wata Yarinya mai shekaru 13 ta tona asirin Mahaifin ta da kuma Kakan ta da suke mata Fyade tsawon shekara biyu 2
Wani labari da muka samu wanda akwai abin tausayi a cikin sa sannan kuma Jama’a da dama sun yi Allah wadai ga Mutumin da ya aikata laifin da kowa yayi mamaki.
Wata Yarinya :Yar shekara goma sha uku 13 ta bayyana cewa, tsawon shekaru kenan Mahaifinta da kuma Kakanta wanda shi ya haifi Baban ta suna yi mata Fyade, wanda Yarinyar tayi kankantar da zasu aikata mata wannan mummunan abin.
Rahotanni daga jihar Osun sun bayyana cewar, hukumar NSCDC ta Jihar ta kama mahaifin wata yarinya mai shekara goma sha uku 13, da kuma kakan ta wanda suka yi mata fyade.
Mai magana da yawun shugaban hukumar Mr Adigun Daniel shi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin ga manema labarai, inda ya bayyana cewar tun bayan da yarinyar tayi korafi a ranar Juma’a aka kama wadanda akezargi.
Wata makwafciyar su ita ce ta kai korafi wajen Jami’an tsaro ta bayyana cewa, yarinyar ta kai mata korafi akan abin da Mahaifin ta tare da Kakan ra suke aikata mata bayan da aka binciki yarinyar sai ta tabbatar da hakan, tare da cewar kusan shekaru biyu kenan suna yin lalata da ita.
Allah yashiryemu,irin masu aikata wannan laifuka Allah yasa sutuba sudaina
Masha Allah