‘Yan Sandan Kano sun yi nasarar kama kasurgumin barawon Keke Napep Aljan tare da abokin sa wanda suke tarewa hanya suke fashi
Rundunar Yan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da cafkekasurgumin barawon babur mai kafa uku wato Keke Napep, wanda a kafi sani da adaidaita sahu a Jihar Kano.
Barawo mai suna Sabitu Ibrahim wanda aka fi sani da Aljan dan kimanin shekaru 18, daga garin Kaburma Yan Daddawa cikin karamar hukumar Dawakin Tofa wanda ke Jihar Kano.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Asabar da daddare gungun yan sanda na sashin Kan kace kwabo wanda rundunar ta ke kira da, Operation Puff Ada karkashin jagorancin SP Buba Yusuf sune suka samu nasarar kama Aljan darawon Keke Napep din.
Abdullahi Haruna Kiyawa ya kara da cewa: An kama shi ne da wani babur mai kafa uku wanda ya ke dauke da lamba GRR77QA da kuma lambar KAROTA KMC 1106.
Sannan ya kara bayyana cewa: Sunan Aljan na cikin jerin sunayen masu laifi da rundunar ke nema ruwa a jallo Kiyawa wanda yake da mukamin DSP, ya kara bayyana cewa a yayin binciken kwakwaf Aljan ya amsa cewa tabbas ya hada baki da wani suka tare wani matukin babur mai kafa uku a Dorayi.
Ya kara da cewa: Aljan ya bada bayanin cewa bayan sun tare matukin babur mai kafa ukun sai suka yi amfani da waya suka shake wuyan shi da niyyar su hallaka shi, amma Allah Ya taimake shi ya kufce ya gudu da raunuka a jikinsa.
Abdullahi Haruna Kiyawa ya kara da cewa: Bayan nan sai Aljan da abokin sa suka tsere da wannan babur din, inda ya kara da cewa wannan babur din mai kafa uku aka kama shi.
Abdullahi Kiyawa yace: Bayan an fadada bincike na siri sai a ka kamo wani Abdullahi Sulaiman mai shekaru 28 dan unguwar Gwale da kuma Abubakar Muhammed mai shekaru 21 dan unguwar Hausawa duk a birnin Kano, bisa zargin su da siyan wasu sassa na babur din da Aljan ya sato da kuma wani babur mai lamba FGE212QX sai kuma lambar KAROTA 4636 KMC da aka same su a tare dasu.
Kiyawa ya bada lambar waya 08105359575 ga wadan da aka sace musu wadan nan baburan da su tuntubi rundunar, ko kuma su tuntubi kakakin kaitsaye.
Kwamishinan Yan Sandan jihar Sama’ila Shu’aibu Dikko ya godewa al’ummar jihar Kano baki daya bisa gudum mawar da suke badawa tare da yin addu’a, da kuma bada kwarin gwiwa tare goyon baya da suke basu sannan kuma ya bukaci a cigaba da basu hadin kai wajen gudanar da ayyukan su.