Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna zata kori Malaman Makaranta 233 wanda ake zargin su da gabatar da takardun bogi

Gwamnatin Kaduna zata kori malaman makaranta 233.

Advertising

Hukumar ilimin bai daya ta Jhar Kaduna zata kori malamai Makaranta dari biyu da talatin da uku 233, wanda ake zargi sun gabatar da takardun makaranta na bogi.

A cikin jawabin Shugaban hukumar mai suna Tijjani Abdullahi da gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya wallafa a Facebook yana mai cewa, an tantance takardun malamai bari hudu da hamsin da daya 451 ta hanyar tuntubar makarantun da malaman suka yi ikirarin sun yi.

Shugaban ya kara da yace: Bahasin da makarantu 13 suka bayar ya nuna malamai dari biyu da talatin da uku 233 takardun jabu suka gabatar.

Advertising

Sannan ya kara da cewa: Daya daga cikin makarantar da aka turawa takardun malaman ta nesanta kanta da shedar karatu dari biyu da goma sha biyu 212 daga cikin dari biyu da talatin da uku 233.

Don haka hukumar zata kori malamai dari biyu da talatin da uku 233 da suka gabatar da takardun makaranta na jabu, sannan kuma za’a gabatar da takardun su ga ma’aikatar shari’a domin fuskantar hukunci.

Bayan haka Hukumar tace zata cigaba da tantance sahihan takardun malaman Jihar a matsayin daya daga cikin matakan da gwamnatin Kaduna ke dauka domin farfado da ilimi.

Hukumar ta kuma kara da cewa: zata yi wa malaman Jihar 12,254 jarabawar gwaji da horo wanda za’a fara daga watan Janairun 2022.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button